Open Bible Stories Home

37. Yesu Ya Tada Li'azaru Daga Mattattu

Labarin LMT daga Yahaya 11:1-46

Wata rana, Yesu ya samu saƙo cewa Li’azaru yana rashin lafiya ƙwarai. Li’azaru da ƴanuwansa mata biyu, Maryamu da Marta, abokan Yesu ne. Da Yesu ya ji wannan labarin, ya ce, “Wannan cutar ba za ta ƙare ba har mutuwa, amma domin ɗaukakar Allah ne.” Yesu yana ƙaunar abokansa, amma ya jira inda yake har kwana biyu.

Bayan kwana biyu sun wuce, Yesu ya cewa almajiransa, “Mu koma Yahudiya.” Amma malam," almajiran suka amsa, “Ba da daɗewa ba mutanen garin sun nemi su kashe ka!” Yesu ya ce, “Ɗan uwanmu Li’azaru ya yi barci, kuma dole in tashe shi.”

Almajiran Yesu suka amsa suka ce, “Malam, in Li’azaru ya yi barci, ke nan zai samu lafiya.” Sai Yesu ya ce masu a sake, “Li’azaru ya mutu. Ina da farin ciki da ba na nan, domin ku gaskanta da ni.”

Da Yesu ya iso garin Li’azaru, Li’azaru ya yi kwana uku da rasuwa. Marta ta tafi tarbenshi, kuma ta ce, “Malan, inda kana nan, da ɗan uwana bai mutu ba. Amma na tabbata Allah zai baka duk abin da ka tambaye shi.”

Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne tashin mattatu da kuma rai. Duk wanda ya gaskanta da ni zai rayu koda ya mutu. Duk wanda ya gaskanta da ni ba zai ƙara mutuwa ba. Kun gaskanta da wannan?” Marta ta amsa, “I, Malam! Na gaskanta kai ne Almasihu, Ɗan Allah.’”

Sai Maryamu ta zo. Ta faɗi a ƙafafuwan Yesu ta ce, “Malam, inda kana nan, ɗan uwana da bai mutu ba.” Yesu ya tambaye su, “Ina ku ka sa Li’azaru?” Suka ce masa, “Cikin kushewa. Zo ka gani.” Sai Yesu ya yi kuka.

Kushewar kogone a rufe da dutse a gaban wurin buɗewa. Da Yesu ya iso kushewar, ya ce masu, “Ku ture dutsen.” Amma Marta ta ce, “Ya yi kwana uku da mutuwa. Ya riga ya ruɓe.”

Yesu ya amsaya ce, “Ba na faɗa maku za ku ga ɗaukakar Allah inda kun gaskanta da niba?” Sai suka ture dutsen.

Sai Yesu ya ɗaga kai sama ya ce, “Uba, na gode da ka saurare ni. Na san kullum kana ji na, amma ina faɗin wannan domin dukan waɗannan mutane da ke tsaye a nan, don su tabbata kai ka aiko ni.” Sai Yesu ya yi ƙara, “Li’azaru, fito waje!”

Sai Li’azaru ya fito! Yana sanye da tufafin kabari. Yesu ya ce mas,:“Ku taimake shi ya fiɗa waɗannan kayan na kabari, kuma ku sake shi! Da yawa daga Yahudawa suka gaskanta da Yesu domin al’ajabai da ya yi.

Amma shugabanin addinin Yahudawa sun cika da kishi, sai suka taru wuri ɗaya don su tsara yadda suke iya kashe Yesu da Li’azaru.

Sura mai zuwa