Open Bible Stories Home

31. Yesu Yana Tafiya Bisan Ruwa

Labarin LMT daga Matiyu 14:22-33; Markus 6:45-52; Yahaya 6:16-21

Sai Yesu ya faɗawa almajiran su shiga cikin jirgin ruwa, kuma su ƙetara zuwa wancan shashen tafkin sa’ad da yake watsar da taron. Bayan da Yesu ya salami taron jama’a, ya hau dutse domin addu’a. Yesu shi kaɗai ne can, kuma ya yi addu’a har farin dare.

Lokacinan almajiran suna tuƙa jirgin ruwansu, amma can cikin dare sun kai tsakiyar tafkin kaɗai. Suna tuƙi da wahala saboda iska tana busawa da ƙarfi gaba da su.

Sai Yesu ya ƙare addu’a, kuma ya tafi wurin almajiran. Ya yi tafiya bisan ruwan tafkin zuwa jirgin ruwan!

Almajiran suka ji tsoro sarai da suka ga Yesu, domin sun yi tsamani suna ga fatalwa ne. Yesu ya sani sun tsorota, sai ya kira su ya ce, “Kadda ku ji tsoro. Ni ne!”

Sai Bitrus ya cewa Yesu, “Malam, in kaine, umurce ni in zo gare ka bisan ruwa.” Yesu ya amsawa Bitrus, “Zo!”

Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwa, kuma ya fara tafiya bisan ruwa. Amma bayan ya yi tafiya wuri kaɗan, ya juya idanunsa baya, kuma ya fara kallon igiyoyin ruwa da iska mai ƙarfi.

Sai Bitrus ya razana, kuma ya fara lumewa cikin ruwa. Ya yi kira, “Malam, ka cece ni!” Yesu ya je nan da nan ya kama shi. Sai ya cewa Bitrus, “Kai mutum mai ƙanƙanuwar bangaskiya, me ya sa ka yi shakka?”

Da Bitrus da Yesu suka isa cikin jirggin ruwan, iska ya tsaya nan da nan, kuma ruwa ya kwanta. Almajiran suka yi mamaki. Suka yabi Yesu suna cewa,“Gaskiya kai Ɗan Allah ne.”

Sura mai zuwa