Isra’ilawa sun cika da murna da barin Masar. Sun zama ƴantattu, sun kama hanya zuwa ƙasar alkawali! Masarawa sun ba Isra’ilawa duk abin da suka tambaye su, har da zinariya da azurfa da duk abubuwa masu tsada. Waɗansu mutanen wasu kabilu suka gaskanta da Allah, suka ka kwa raka Isra’ilawa yayin da suka fita daga Masar.
Allah ya bida su da al’amudin girgije da yake jagoransu da rana, kuma da dare sai ya zama al’amudin wuta. Allah yana tare da su kulluyaumin, ya kuma jagorance su lokacin tafiyarsu. Duk abin da za su yi shi ne su bi shi.
Bayan ɗan lokaci, Fir’auna da mutanensa suka canza tunaninsu, kuma sai suka so su maido da Isra’ilawa su zama bayinsu hallo. Allah ya sa Fir’auna ya zama mai taurin kai domin mutane su gane da cewa shi ƙaɗai ne Allah na gaskiya, shi ne Yahweh, ya kuma fi Fir’auna da allolinsa iko.
Sai Fir’auna da sojojinsa suka tafi bin bayan Isra’ilawa don su maida su bayi hallo. Da Isra’ilawa suka ga rundunar sojojin Masar suna bin bayansu, sai suka gani sun kamu a tarko tsakanin sojojin Fir’auna da Bahar Maliya. Sun firgita sosai, kuma suka yi ƙara, “Don mi muka fito daga Masar? Za mu mutu!”
Musa ya faɗa wa Isra’ilawa, “Kada ku ji tsoro! Allah zai yi yaƙi dominku yau, ya kuma cece ku.” Sai Allah ya cewa Musa, “Gaya wa mutane su kusato Bahar Maliya.”
Sai Allah ya gusa al’amudin girgije, ya sa shi tsakanin Isra’ilawa da Masarawa domin kada Masarawan su ga Isra’ilawa.
Allah ya cewa Musa ya ɗaga hannunsa bisan bahar ya raba ruwayen. Sai Allah ya sa iska ya ture ruwan cikin Bahar Maliya zuwa hagum da dama, haka sai hanya ta samu tsakiyar bahar.
Isra’ilawa suka ratsa tsakiyar bahar bisa busasshiyar ƙasa da duk ruwaye a kowane gefen.
Sai Allah ya gusa girgijen gaba, ba bisa kan hanyar ba, don Masarawa su gani Isra’ilawa sun kuɓuta. Masarawan sun ƙudurta su bi bayansu.
Sai suka bi bayan Isra’ilawan bisa hanyar cikin bahar, amma Allah ya tsorota Masarawan, ƙafafun karusansu suka kafe. Suka yi ƙara, “Ku gudu! Allah yana kokawa domin Isra’ilawa!”
Bayan da Isra’ilawa suka kai wancen sashen teku lafiya, Allah ya cewa Musa ya sake ɗaga hannunsa kuma. Da ya yi biyayya, ruwa ya faɗo kan rundunar sojojin Masar, ya kuma koma wurinsa na da. Dukan rundunar sojojin Masar suka ciyu.
Da Isra’ilawa suka ga Masarawan sun mutu, sai suka gaskanta da Allah da kuma Musa annabin Allah.
Isra’ilawa suka ka yi farin ciki sosai sabili da Allah ya cece su daga mutuwa, kuma daga bauta! Yanzu sun ƴantattu ne domin sun bauta ma Allah. Isra’ilawa sun raira waƙoƙin yabo da dama domin ƴancin da suka samu, kuma yabon Allah domin ya cece su daga rundunar sojojin Masar.
Allah ya umurci Isra’ilawa su yi Idin Ƙetarewa kowace shekara domin su tuna da yadda Allah ya basu nasara kan Masarawa, ya kuma cece su daga bauta. Suka yi idin ta wurin kashe ɗan rago maras aibu, suka ci shi da gurasa maras yis.