Open Bible Stories Home

10. Alloba Goma

Labari LMT daga Fitowa 5-10

Musa da Harouna suka je wurin Fir’auna suka ce, “Ga abin da Allah na Isra’ila ya ce, ‘Bar mutane na su fita daga ƙasarka!’” Fir’auna bai jin su ba. Maimakon ya bar Isra’ilawa su tafi, sai ƙara nauyin aikinsu.

Fir’auna ya ƙi ya bar mutanen su tafi, sai Allah ya aiko alloba goma a Masar. Ta wurin wannan allobar, Allah ya nuna wa Fir’auna ya fi shi iko da shi da dukan allolin Masar.

Allah ya maida ruwan kogin Nilu jini, amma duk da wannan Fir’auna ya ƙi barin Isra’ilawa su tafi.

Allah ya aiko da kwaɗi a Masar. Fir’auna ya roƙi Musa ya kawas da kwaɗin. Amma bayan da kwaɗin sun mutu, Fir’auna ya taurare zuciyarshi, ya ƙi ya bar Isra’ilawa su fita daga Masar.

Sai Allah ya aiko allabar kwarkwata. Ya kuma aiko kwarkwatar ƙudaje. Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce masu idan sun tsaida allobar, Isra’ilawa suna iya fita daga Masar. Da Musa ya yi addu’a, Allah ya ɗauke duk ƙudaje daga Masar. Amma Fir’auna ya ƙara taurare zuciyarsa ya hana su fita.

Sai kuma Allah ya sa dukan dabbobin Masarawa rashin lafiya da mutuwa. Duk da wannan Fir’auna ya taurare zuciyarsa, ya ƙi ya bar Isra’ilawa su tafi.

Sai Allah ya ambaci Musa ya watsa toka cikin iska a gaban Fir’auna. Da ya yi haka nan sai marurai masu zafin ciwo suka fito a jikin masarawa, banda Isra’ilawa. Allah ya taurara zuciyar Fir’auna, kuma Fir’auna bai yarda Isra’ilawa su fita ba.

Bayan wannan, Allah ya aike da ƙanƙara da ta hallaka yawancin anfanin gonar Masar da duk mutanen da ke waje a lokacin. Fir’auna ya kira Musa da Haruna ya ce masu, “Na yi zunubi. Sai ku tafi.” Sai Musa ya yi addu’a, sai ƙanƙara ta fasa faɗowa.

Amma Fir’auna ya ƙara zunubi, ya kuma taurare zuciyarsa. Ya ƙi ya bar Isra’ilawa su tafi.

Sai Allah ya sa ɗumbun fara suka faɗo kan Masar. Fara sun cinye duk ganyen da ƙanƙara ba ta hallaka ba.

Sai kuma Allah ya aiko da duhu har kwana uku. Duhun ya yi yawa har da Masarawa basu iya barin gidajensu ba. Amma akwai haske a inda Isra’ilawa suke.

Duk da haka bayan waɗannan allobai tara, Fir’auna ya ƙi ya saki Isra’ilawa su tafi. Tun da Fir’auna ba ya ji, Allah ya ƙadara ya aika alloba ta ƙarshe. Wannan za ta canza tunaninsa.

Sura mai zuwa