Open Bible Stories Home

4. Alkawalin Allah Ga Ibrahim

Labarin LMT daga Farawa 11-15

Shekaru da yawa bayan ambaliyar ruwa, mutane sun riɓanɓanya a duniya, suna kuwa magana cikin harshe guda. Ba su je suka cika duniya ba, amma sun tsaya wuri guda sun gina birni.

Sun cika da farha, ba su kula da zancen Allah ba. Sai suka fara gina doguwar hasumiya don su kai sama. Allah ya gani idan dai sun ci gaba da taraya cikin yin mugunta, za su lalace cikin zunubensu.

Sai Allah ya dagula harshensu cikin harsuna dabam dabam. Ya kuma warwatsa su ko’ina cikin duniya. Birnin da suka fara ginawa sunansa Babila, ma’ana “ruɗani.”

Shekaru ɗaruruwa suka wuce, Allah ya yi magana da wani mutum mai suna Abram. Allah ya ce masa, “Ka fita daga ƙasarka da danginka, ka je wata ƙasa da zan numa maka. Zan albarkace ka in kuma maishe ka al’umma mai girma. Zan albarkaci waɗanda suka albarkace ka, amma zan la’anta waɗanda suka la’antaka. Dukan al’umman duniya za su samu albarka sabili da kai.”

Sai Abram ya yi biyayya ga Allah. Ya ɗauki matarsa Saraya, tare da dukan barorinsa da dukan mallakarsu, ya tafi ƙasar da Allah ya gwada masa, ƙasar Kana’ana.

Da Abram ya iso ƙasar Kana’ana sai Allah ya ce, “Duba kewaye da kai. Zan baka, kai da zuriyarka dukan ƙasar da kake gani gado.” Sai Abram ya zauna cikin ƙasar.

Wata rana Abram ya gamu da Malkisadik, firist na Allah Maɗaukaki. Malkisadik ya albarkaci Abram ya ce, “Bari Allah Maɗaukaki wanda ya yi sama da ƙasa ya sa wa Abram albarka.” Sai Abram ya ba Malkisadik zaka na dukan dukiyarsa.

Shekaru da dama sun wuce amma Abram da Saraya ba su haifu ba. Allah ya yi magana da Abram ya yi masa alkawalin samun ɗa da zuriyar mai yawa kamar taurarin sama. Abram ya gaskanta da wannan alkawali. Allah kuwa ya lasafta wannan adalci ne a gare shi.

Sai Allah ya ɗauki ƙuduri da Abram. Ƙuduri sharaɗi ne tsakanin sashe biyu. Allah ya ce, “Zan baka ɗa daga cikinka. Na ba zuriyarka ƙasar kana’ana.” Amma Abram bai haifu ba tukuna.

Sura mai zuwa