Wata rana, Yesu ya ɗauki uku daga cikin almajiransa, Bitrus, Yakubu da Yahaya tare da shi. (Almajirin mai sunan Yahaya ba shine ba Yahaya mai baftisma.) Suka tafi sama bisan dutsi don su keɓe su yi addu’a.
Sa’adda Yesu yake addu’a, fuskarsa ta zama da haske kamar rana, kuma tufafinsa suka zama farare kamar haske, farare fiye da kowane a duniya yake iyawa.
Sai Musa da annabi Iliya suka bayyana gareshi. Waɗannan mutane sun rayu a duniya shekaru ɗaruruwa da suka wuce. Sun yi magana da Yesu a kan mutuwarsa, da za ta faru ba da daɗewa ba a Urshalima.
Yayin da Musa da Iliya suke magana da Yesu, Bitrus ya ce wa Yesu, “Yana da kyau mu kasance a nan. Bari mu yi runfa uku, ɗaya dominka, ɗaya don Musa, kuma ɗaya domin Iliya.” Bitrus bai san abin da yake cewa ba.
Sa’ad da Bitrus yake magana, hadiri mai hasken gaske ya sauko ya kewaye su, kuma murya daga sama ta ce, “Wannan ɗana ne ƙaunatace. Ina farin ciki da shi. Ku saurare ni.” Almajiran uku suka firgita, suka faɗi a ƙasa.
Sai Yesu ya taɓa su ya ce, “Kada ku ji tsoro. Ku tashi.” Da suka duba kewaye da su, babu kowa sai Yesu kaɗai.
Yesu da almajiran uku suka koma gida daga dutsen. Sai Yesu ya ce masu, “Kada ku faɗawa kowa abin da ya faru a nan tukuna. Zan mutu ba da daɗewa ba, kuma zan komo rayayye. Bayan wannan, kuna iya faɗawa mutane.”