Bayan shekaru da dama, loton da Yakubu ya zama tsohon mutum, ya aike da ƙaunatacen ɗansa Yusufu, ya duba ƴan’uwansa da suke kiwon garkensu.
Ƴan’uwan Yusufu suna kishinshi sabili da ubansu ya fi ƙaunarsa, kuma sabili da Yusufu ya yi mafalki zai zama mai ikonsu. Da Yusufu ya zo wurin ƴan’uwan sai suka kama shi suka saiyar da shi ga masu saiyar da bayi.
Kafin ƴan’uwan Yusufu su koma gida sai suka cira rigar Yusufu, suka jiƙa ta da jinin akuya. Sai suka gwada wa uban rigar don ya yi zaton cewa da dabbar daji ta kashe Yusufu. Yakubu ya yi baƙin ciki sosai.
Masu sayar da bayi suka kai Yusufu Masar. Masar, ƙasa ce mai faɗi, mai mulki, tana jikin ruwan Nilu. Masu sayar da bayi suka saida Yusufu kamar bawa ga wani mai arziki, ma’aikacin gwamnati. Yusufu ya bauta mashi da kyau, sai Allah ya albarkace shi.
Matar maigidanshi ta jaraba ta kwana da Yusufu, amma Yusufu bai yarda ya yi ma Allah zunubi haka ba. Ta husata sai ta zargi Yusufu har an kama shi a kurkuku. Ko a kaso Yusufu ya dogara ga Allah, sai Allah ya albarkace shi.
Bayan shekara biyu, Yusufu yana dai cikin kurkuku, ko da yake maras laifi ne. Wani dare, Fir’auna, wanda masarawa ke kira sarkinsu, ya yi mafalki biyu da suka tada hankalinsa. Ba mashawartansa ko guda da ya iya bashi fasarar mafalkin.
Allah ya baiwa Yusufu fasarar mafalkai, sai Fir’auna ya sa aka fito da Yusufu daga kaso. Yusufu ya fasarta mafalkai ya ce, “Allah zai aiko da shekara bakwai na yalwar girbi, kuma bayansu shekara bakwai na yunwa.”
Fir’auna ya ƙasaita sosai da Yusufu, sai ya naɗa shi mutum na biyu mai iko a cikin dukan Masar.
Yusufu ya umurci mutane su tanada abinci da yawa lokacin yalwar girbi shekara bakwai. Sai Yusufu ya sayar wa mutane abinci lokacin da shekara bakwai na yunwa suka fara. Ta haka abincin mutane ya isa.
Yunwar na da tsanani ba cikin Masar ƙaɗai ba, har a Kana’ana inda Yakubu da iyalinsa suke zaune.
Sai Yakubu ya aike da manyan ƴaƴansa Masar don sayan abinci. Ƴan’uwan basu gane Yusufu ba da suka tsaya gabansa wurin sayan abinci. Amma Yusufu ya gane su.
Bayan ya gwada ƴan’uwansa ya gani ko sun canza hali, Yusufu ya ce masu, “Ni ne ɗanuwanku Yusufu! Kada ku ji tsoro. Kun yi zaton yin mugunta da ku ka sayar da ni kamar bawa, amma Allah ya yi anfani da wannan ya yi alheri! Ku zo ku zauna a Masar sai in taimakeku, ku da iyalinku.”
Da ƴan’uwan Yusufu suka koma gida, suka ba ubansu Yakubu, labarin Yusufu yana da rai, ya yi farin ciki.
Koda yake Yakubu ya tsufa, ya ƙaura zuwa Masar da dukan iyalinsa, sun kuma zauna a can. Kafin Yakubu ya mutu ya albarkaci kowane daga ɗiyansa maza.
Rantsuwar alkawarai da Allah ya baiwa Ibrahim suka hau kan Ishaƙu, kuma Yakubu, kuma kan ƴaƴa goma sha biyu na Yakubu da iyalensu. Zuriyar sha biyun su ne suka zama kabilu sha biyu na Isra’ila.