Open Bible Stories Home

24. Yahaya Ya Yi Wa Yesu Baftisma

Labrin LMT daga Matiyu 3; Markus 1:9-11; Luka 3:1-23

Yahaya, ɗan Zakariya da Alisabatu, ya girma, kuma ya zama annabi. Ya zauna cikin jeji, ya ci zumar daji da fara, kuma yana sa tufafin fatar raƙumi.

Mutane da yawa zun zo cikin jeji su saurari Yahaya. Ya yi masu wa’azi cewa, “Ku tuba, gama mulkin Allah ya yi kusa!”

Da mutane suka ji saƙon Yahaya, da yawa daga cikinsu suka tuba daga zunubensu, kuma Yahaya ya yi musu baftisima. Shugabani adinai da yawa suka zo Yahaya ya yi musu baftisima, amma ba su tuba ba ko su faɗi laifinsu.

Yahaya ya cewa shuganin adinai, “Ku macizai masu dafi! Ku tuba ku canza tafiyarku. Duk icen da ba ya bada ƴaƴa, za cire shi, kuma a jefa shi cikin wuta.” Yahaya ya cika abin da annabawa suka faɗa, “Duba zan aike da masinja na a gaban ka, zai shirya wuri dominka.”

Wasu Yahudawa suka tambayi Yahaya in shi ne Almasihu. Yahaya ya amsa ya ce, “Ba ni ba ne Almasihu, amma akwai mai zuwa bayana, shi babba ne da ban isa ba in ɓalle takalminsa.”

Ranar gobe, Yesu ya zo Yahaya ya yi masa baftisima. Da Yahaya ya gan shi ya ce, “Duba! Ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya.”

Yahaya ya cewa Yesu, “Ni ba isa ba in yi maka baftisima. Kai na ya kamata ka yi mini baftisma.” Amma Yesu ya ceM, “Ka yi mini baftisma domin daidai ne abin da ya kamata.” Sai Yahaya ya yi masa baftisma, ko da yake Yesu bai taɓa yin zunubi ba.

Da Yesu ya fito daga ruwan baftisma, Ruhun Allah ya sauko a kan shi cikin kamannin kurciya, ya zauna bisansa. A wannan lokacin, muryar Allah ta yi magana daga sama cewa, “Kai ne ɗana ƙaunatace, Ina kwa jin daɗinka.”

Allah ya faɗa wa Yahaya, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko ya zauna a kan wani da za yi wa baftisma. Wannan mutum Ɗan Allah ne.” Amma sa’ad da Yahaya ya yi wa Yesu baftisma, ya ji Allah Uba ya yi magana, ya ga Allah Ɗa, wato Yesu, kuma ya ga Ruhu Mai Tsarki.

Sura mai zuwa