Open Bible Stories Home

7. Allah Ya Albarkaci Yakubu

Labarin LMT daga Farawa 25:27-33:20

Sa’ad da samarin suka girma, Yakubu ya fi son zama a gida, amma Isuwa yana son farauta. Rifkatu ta fi ƙaunar Yakubu, amma Ishaƙu ya fi ƙaunar Isuwa.

Wata rana da Isuwa ya dawo daga farauta, ya ji yunwa sosai. Isuwa ya cewa Yakubu, “Dan Allah ka bani ɗan abinci da ka dafa.” Yakubu ya amsa ya ce, “Sai ka bani matsayinka na ɗan fari.” Sai Isuwa ya baiwa Yakubu matsayinshi na ɗan fari. Sa’annan Yakubu ya ba shi abinci.

Ishaƙu yana so ya sa wa Isuwa albarka. Amma kafin ya yi Rifkatu da Yakubu suka yaudare shi ta wurin sawa Yakubu kanbacin Isuwa. Ishaƙu ya tsufa, kuma makafo ne. Sai Yakubu ya sa tufar Isuwa, ya kuma yi sutura da fatar akuya a wuyansa da hanuwansa.

Yakubu ya taho wurin Ishaƙu ya ce, “Ni ne Isuwa. Na zo domin ka sa mini albarka.” Da Ishaƙu ya shafi gashin akuya, ya kuma shinshina kayan jikin, sai ya yi tsammani Isuwa ne, sai ya sa masa albarka.

Isuwa ya husata domin Yakubu ya sace masa matsayinsa na ɗan fari da kuma albarkarsa. Sai ya ƙudura ya kashe Yakubu bayan mutuwar ubansu.

Amma Rifkatu ta ji labarin ƙudurin Isuwa. Sai ita da Ishaƙu suka aiki Yakubu nesa zuwa gidan ubanninta.

Yakubu ya zauna a gidan ƴan’uwan Rifkatu shekaru da yawa. A lokacin nan ya yi aure, ya kuma haifi ƴaƴa maza goma sha biyu da ɗiya mace guda. Ubangiji ya ba shi arziki da yawa.

Bayan shekara ashirin a waje da gidansa na Kana’ana, Yakubu ya koma tare da iyalinsa, da barorinsa, da dukan garkunan dabbobinsa.

Yakubu ya cika da tsoro da yawa domin yana tsammani Isuwa yana so ya kashe shi har yanzu. Sai ya aike da garkunan dabbobi da yawa kyauta domin Isuwa. Baran da ya kawo da kyautar ya cewa Isuwa, “Baranka Yakubu yake ba ka waɗannan dabbobin. Yana zuwa da sauri.”

Amma Isuwa ya riga ya gafurtawa Yakubu, sai suka ji daɗin sake saduwa. Yakubu ya zauna hankali kwance a Kana’ana. Sai Ishaƙu ya rasu, Yakubu da Isuwa suka binne shi. Alkarin da Allah ya yi wa Ibrahim ya koma daga kan Ishaƙu zuwa kan Yakubu.

Sura mai zuwa