Open Bible Stories Home

13. Alkawalin Allah ga Isra'ila

Labarin LMT daga Fitowa 19-34

Bayan da Allah ya bida Isra’ilawa ta cikin Bahar Maliya, ya bida su cikin jeji zuwa dutsen Sinai. A wannan wurin ne Musa ya ga al’amudi mai cin wuta. Mutanen suka yi zango a ƙasan dutsen.

Allah ya cewa Musa da mutanen Isra’ila, “In kun yi mini biyayya, kun kuma riƙe alkawarina, za ku zama nawa masu tamani, mulkin firistoci, al’umma mai tsarki.”

Bayan kwana uku, bayan da mutane suka shirya kansu cikin ruhaniya, Allah ya sauko bisa dutsen Sinai da tsawa, da walƙiya, da hayaƙi, da kakaki may babban ƙara. Musa ƙaɗai ne aka yardar ma ya je saman dutsen.

Sai Allah ya basu alkawali, “Ni ne Yahweh, Allahnku, da ya cece ku daga bauta a Masar, Kar ku bautawa waɗansu alloli.”

“Kada ku yi kumaka, kada ku bauta masu, domin Ni ne Yahweh, Ina da kishi. Kada ku yi anfani da sunana a banza. Ku kiyaye ranar Asabar da tsarki. Ke nan ku yi dukan aikinku a kwana shida, kwana na bakwai ranar hutu ce da tunawa da Ni.

“Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka. Kada ka yi kisan kai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka yi ƙarya. Kada ka yi fasiƙanci da matar maƙobcinka ko ka yi ƙyashin gidansa ko kayansa.

Sai Allah ya rubuta wannan dokoki goma bisan alloli biyu na dutse ya kuma baiwa Musa. Allah ya kuma bada waɗansu dokoki kamar haka. Idan mutane sun yi biyayya da dokokin, Allah ya yi alkawalin sa masu albarka da kuma kare su. Idan sun ƙi biyayya Allah zai hore su.

Allah ya kuma ba Isra’ilawa umurni yadda za su gina alfarwa. Ana kiranta alfarwa taruwa, tana da ɗaki biyu a rabe. Babban Firist kaɗai yake iya shiga cikin ɗaki bayan labule domin nan ne Allah yake zaune.

Duk wanda ya yi rashin biyayya ga dokokin Allah, sai ya kawo dabba wurin bagadi gaban alfarwa ta taruwa don hadaya. Firist zai yanke dabbar, ya kuma ƙone ta a bisan bagadin. Jinin dabbar da aka miƙa hadaya ya shafe zunubin mutumin a gaban Allah. Allah ya zaɓi ɗan uwan Musa, Haruna, da zuriyarsa su zama firistoci.

Dukan mutane suka yarda su yi biyayya da dokokin da Allah ya basu, su bauta ma Allah kaɗai, su zama keɓaɓɓun matanensa. Amma bayan lokaci ƙaɗan da wannan alkawalin, sai suka yi zunubi.

Kwana da yawa Musa yana kan dutsen Sinai yana magana da Allah. Mutanen sun gaji da jiran shi ya komo, sai suka kawo zinariya wurin Haruna suka tambaye shi ya gina gumki dominsu.

Haruna ya yi gumkin zinariya kamar ɗan maraƙi. Sai mutanen suka fara bauta masa, suna yi masa hadaya! Allah ya husata sai ya yi ƙudurin ya hallaka su. Amma Musa ya yi addu’a saboda su, sai Allah ya ji roƙonshi ya fasa hallaka su.

Da Musa ya sauko daga dutsen ya ga gumkin, ya husata sosai, sai ya fashe allolin waɗanda suke da dokoki goma a rubuce.

Sai Musa ya kwankatse gumki, ya zama gari, ya watsar da garin cikin ruwa, ya kuma sa mutanen suka sha ruwan. Allah ya aike da alloba bisan mutanen, da yawa suka mutu.

Musa ya hau dutsen kuma, ya yi addu’a Allah ya gafartawa mutanen. Allah ya amshi addu’ar, ya huma gafarta masu. Musa ya rubuta dokokin goma a kan sababbin allolin dutse kanbacin karyayyun. Musa ya sauko daga dutsen ɗauke da Dokokin Goma bisa sabin alloli. Sai Allah ya bida Isra’ilawa daga dutsen Sinai zuwa ƙasar alkawali.

Sura mai zuwa