A ƙarshe sai lokaci yayi da Isra’ilawa za su shiga Kan’ana ƙasar alkawali. Joshuwa ya aiki ƴan leƙen asiri biyu garuruwan Kan’aniyawa da suke kewaye da katanga mai ƙarfi. Cikin wannan gari akwai wata karuwa mai sunan Rahab da ta ɓoye ƴan leƙen asirin, ta kuma taimake su su tsira. Ta yi wannan domin ta gaskanta da Allah. Sun yi ƙudurin taimakon Rahab da iyalinta lokacin da Isra’ilawa za su hallaka Yeriko.
Sai da Isra’ilawa suka ratsa kogin Urdun, suka shiga ƙasar alkawali. Allah ya cewa Joshuwa, “Firist su shiga gaba.” Da firistoci suka sa ƙafafu cikin kogin Urdun, sai ruwan ya tsaya da hucewa, Isra’ilawa suka ƙetara zuwa gefen bisan busasshiyar ƙasa.
Bayan da mutanen suka ratsa kogin Urdun, Allah ya gayawa Joshuwa yadda za su yaƙi birnin Yeriko. Mutanen su ka yi wa Allah biyayya. Kamar yadda Allah ya faɗa masu, sojojin da firistoci suka kewaye birnin Yeriko sau guda kowace rana har kwana shida.
Sai a kwana na bakwai, Isra’ilawa suka kewaye garin sau bakwai. Da suka kewaye garin kari na ƙarshe, sojojin suka yi ƙara, firistocin suka busa ƙahoni.
Sai garunan kewaye da Yeriko suka faɗi! Isra’ilawa suka hallaka komi cikin garin kamar yadda Allah ya umurce su. Sun ceci Rahab da iyalinta, sai suka zama cikin Isra’ilawa. Da sauran mutanen Kan’ana suka ji Isra’ilawa sun hallaka Yeriko, suka tsorota suma Isra’ilawa za su faɗa masu.
Allah ya umurci Isra’ilawa kada su yi sulhu da kowace kabila cikin Kan’ana. Amma ɗaya daga cikin kabilar Kan’ana da ake kira Gibenawa suka yi ƙarya, suka cewa Joshuwa su ba na Kan’ana ba ne. Suka tambayi Joshuwa ya yi sulhu da su. Joshuwa da Isra’ilawa ba su tambayi Allah ba daga ina Gibenawan suka fito. Sai Joshuwa ya sasanta da su.
Isra’ilawa sun husata da suka gane da cewa Gibenawa sun ruɗe su, amma sun riƙe alkawalin sulhun da suka masu domin alkawali ne a gaban Allah. Wata rana, sarakunan wata kabilar Kan’ana, Amorawa, suka ji labari Gibenawa sun yi sulhu da Isra’ilawa, sai suka haɗu cikin rundunar sojoji su yaƙi Gibewon. Gibenawa suka aike da saƙo wurin Joshuwa neman taimako.
Sai Joshuwa ya tattara rundunan sojojin Isra’ila, suka kuma yi tafiya dukan dare don su isko Gibenawa. Da asuba sun shammaci sojojin Amorawa sun faɗa masu da yaƙi.
Allah ya yi yaƙi domin Isra’ila wannan rana. Ya ɓikita Amorawa, ya kuma aike da manyan duwatsuna (ƙanƙara) da suka kashe mafi yawa daga Amorawan.
Allah ya kuma sa rana ta tsaya wuri guda cikin sama don Isra’ilawa su samu lokaci isasshe cin yaƙin Amorawa. A wannan rana, Allah ya ci babbar nasara domin Isra’ila.
Bayan da Allah ya ci waɗannan rundunan sojojin da yaƙi, da yawa daga sauran kabilun Kan’ana suka haɗu tare don su yaƙi Isra’ila. Joshuwa da Isra’ilawa suka faɗa su, suka hallaka su.
Bayan wannan yaƙin, Allah ya baiwa kowace kabila ta Isra’ila yankin ƙasa a ƙasar alkawali. Sai Allah ya baiwa Isra’ila kwanciyar hankali bisan dukan iyakansu.
Da Joshuwa ya tsufa, ya kira dukan mutanen Isra’ila gaba ɗaya. Sai Joshuwa ya tunawa mutanen jawabinsu ne su yi biyayya da alkawalin da Allah ya ɗauka da su a Sinai. Mutanen suka ɗauki alkawalin manne wa Allah da dokokinsa.