Da Ibrahim ya tsufa sosai, ɗanshi Ishaƙu ya zama namiji. Sai Ibrahim ya aiki ɗaya daga cikin barorinsa can ƙasar iyayensa domin ya komo da mata don ɗansa Ishaƙu.
Bayan tafiya mai nisa zuwa ƙasar kakannin Ibrahim, Allah ya bida baran zuwa ga Rifkatu. Ita jikanyar ɗan uwan Ibrahim ce.
Rifkatu ta yarda, ta bar iyalinta, ta tafi da baran gidan Ishaƙu. Ishaƙu ya aure ta daga zuwanta.
Bayan tsowon kwanaki, Ibrahim ya mutu sai duk alkawarai da Allah ya yi masa suka koma kan Ishaƙu. Allah ya alkawarta da Ibrahim zai samu babbar zuriya, amma matar Ishaƙu, Rifkatu ba ta iya haifuwa.
Ishaƙu ya yi addu’a domin Rifkatu, sai Allah ya yardar mata ta ɗauki cikin tagwaye. Jarirai biyu suna jayeyya tun cikin cikin Rifkatu. Sai Rifkatu ta tambayi Ubangiji, “Me ke faruwa?”
Allah ya cewa Rifkatu, “Al’umma biyu za su fito daga cikinki. Za su yi jayeyya tsakaninsu, kuma babban zai bauta ma ƙaramin.”
Da Rifkatu ta haifi ɗiyan, babban ya zo da gashi ja-ja, sai suka kira sunanshi Isuwa. Ƙaramin ya fito yana riƙe da diddigen Isuwa, sai suka kira sunansa Yakubu.